Sabon shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya bukaci jigo a jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, da ya ci tuwon girma a matsayinsa na dattijon jam’iyya, kuma ya mayar da wukarsa kube, ya bayar da hadin kan da ya dace, don daidaita al’amuran jam’iyyar.
Sabon shugaban jam’iyyar ta PDP na kasa, ya yi wannan kira ne bayan Sule Lamidon ya yi wata hira da kafar labarai ta BBC inda ya tabo batutuwa da dama ciki har da batun rikicin shugabancin jam’iyyar wanda har ya kai shi ga shigar da kara kotu.
Shugaban PDP ya ce akwai gyara a wasu daga cikin bayanan da tsohon gwamnan na Jigawan ya yi.
A cewar Umar Sani, makusanci ga sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya ce kamata ya yi tsohon gwamnan na Jigawa, ya yi hakuri ya mayar da komai ba komai ba.
