
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da takwaransa na Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, a birnin Brasilia domin tattauna hanyoyin inganta dangantakar diflomasiyya da ci gaban tattalin arziki.
A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, kasashen biyu sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa a fannonin noma, kasuwanci, tsaro, makamashi, ilimi da ma’adinai tun watan Maris 2025.
Taron ya nuni da sabon babi a dangantakar Najeriya da Brazil, inda ake sa ran za a samu karin zuba jari da bunkasar cinikayya tsakanin kasashen.