Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu mutane uku a unguwar Kabuga da ake zargi da tura Alert din bogi bayan da suka sayi mota kirar Mercedes Benz.
Wadanda aka kama sun hada da Ibrahim Tijjani da Jamilu Auwal da Muhammad Nura Dauda.
Wadanda ake zargi sun sayi moto a Gwarinpa dake Abuja akan kudi naira miliyan 75 tare da tura alert din bogi na kudin ga Ibrahim Yahaya.
- Rundunar ’Yan Sanda a Kano Ta Dakile Safarar Abubuwan Fashewa Bayan Bayanai na Sirri
- ’Yan Sanda Sun Yi Gargadi Kan Ta’addanci a Kano
Cikin sanarwar da kakakin rundunar SP Haruna Kiyawa ya fitar ya ce tuni aka kwato motar tare da mika ta ga rundunar ‘yan sanda dake Abuja domin cigaba da bincike.
Ga tattaunawar kakakin ‘yan sandan Kano SP Kiyawa tare da daya daga cikin wadanda aka kama.
SP Haruna Kiyawa ya ce kwamishinan ‘yan sandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya bukaci alumma su cigaba da sanya ido tare da sanar da duk abun da basu gamsu da shi ba ga rundunar.
