Rundunar ‘yansanda a jihar Zamfara ta ce ta yi nasarar kuɓutar da mata da ‘ya’yansu 25 da ‘yanfashin daji suka yi garkuwa da su ranar Juma’a.
Kakakin rundunar a jihar DSP Yazid Abubakar, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Kuraje da ke Gusau babban birnin jihar, inda ‘yanbindigar suka tafi da mata 10 da ‘ya’yansu 15.
A cewar DSP Abubakar Bayan samun kiran gaggawa dakarun haɗin gwiwa na Damba da na Gusau suka ɗunguma zuwa wurin. Tawagar ta bi sawun maharan kuma ta far musu,
Ya ƙara da cewa “hakan ta sa aka yi nasarar kuɓutar da mutanen 25, waɗanda aka kai su Sabon Garin Damba domin tantance su.
Ƙoƙarin jami’an tsaron na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da alhinin sace ɗalibai 25 a jihar Kebbi mai maƙwabtaka, da kuma wasu fiye da 300 a jihar Neja ita ma mai maƙwabtaka da Zamfaran – duka a wannan makon.
