Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wata mata, Rita Ughale, a karamar hukumar Ethiope East, bisa zargin sayar da jaririnta mai watanni biyu kan Naira miliyan 1 da dubu dari 5.
An bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, SP Bright Edafe, ya sanya wa hannu, kuma an aka rabawa manema a Warri ranar Juma’a.
A cewar kakakin ‘yan sandan, a ranar 15 ga Disamba, 2025, wata Rita Ughale, ta bayar da rahoto a sashin ‘yan sandan Ekpan cewa an sace jaririnta mai watanni biyu a lokacin wani fashi yayin da take tafiya a cikin baburin adaidaita sahu.
- ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Da Harsasai 1,000 a Zamfara
- Ƴan Sanda 230 daga Kenya Sun Isa Haiti Don Taimakawa UN
Da samun rahoton, jami’in ‘yan sandan yankin, CSP Labe Joseph, ya fara aikin bincike da ceto jaririn tare da jami’an ‘yan sanda nan take.
Ya ƙara da cewa bayan bincike mai zurfi, mai ƙarar ta amsa laifin sayar da ɗanta mai watanni biyu ga wasu ma’aurata, Osas Omijie mai shekaru 39 da matarsa Judith Omijie mai shekaru 30, kan kuɗi Naira miliyan 1 da rabi.
Sanarwar ta ce Duk mai siyarwa da mai siyan suna hannun ‘yan sanda a halin yanzu, yayin da aka ceto jaririn cikin nasara kuma yana cikin koshin lafiya.
