Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta sanar da kama wasu matasa uku da ake zargin suna da hannu wajen satar yara maza guda biyu a Ƙaramar Hukumar Jere ta jihar.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Sanarwar ta ce waɗanda ake zargin sun haɗa da Abubakar Hassan mai shekaru 19, Modu Aji mai shekaru 18, da Baba Goni Abatcha mai shekaru 18.
An kama su ne a ranar 13 ga watan Disamba, 2025, bisa zargin cewa sun sace yaran a ranar 5 ga watan Disamba, 2025.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya yaba wa jami’an rundunar bisa ƙwazo da jajircewarsu wajen gano tare da kama waɗanda ake zargi.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa bai wa ’yan sanda sahihan bayanai a kan lokaci, domin taimakawa wajen hana aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron al’umma.
CP Naziru Abdulmajid ya tabbatar da cewa bincike kan lamarin na ci gaba da gudana, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
