
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Mansur bisa zargin kashe saurayin ƙanwarsa a lokacin da ya je zance a gidansu.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a kauyen Kunya da ke karamar hukumar Minjibir.
Ya kuma ce, an kama wanda ake zargi domin gudanar da cikakken bincike a sashen da ke kula da manyan laifuka na rundunar.
Rundunar ƴan sanda ta shawarci jama’a da su kasance masu hakuri a cikin dukkan al’amuransu, tare da kai rahoton duk wata matsala ko rikici zuwa ofishin ƴan sanda mafi kusa, domin kauce wa ɗaukar doka a hannu.