Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta samu nasarar ceto yara biyu da aka sace a yankin Tilden Fulani, Ƙaramar Hukumar Toro, tare da cafke wanda ake zargi da aikata laifin.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 23 ga watan Oktoba na shekarar 2025, da misalin ƙarfe 12 na rana, lokacin da wani mai suna Aliyu Hamisu ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Tilden Fulani cewa ‘ya’yansa biyu — Halima Hamisu mai shekaru 12 da Mohammed Aliyu Hamisu mai shekaru 6 — sun bace yayin da suke jiran motar makaranta a bakin titi.
Bincike na farko ya nuna cewa wani mutum a cikin keke Napep ne ya ɗauke su.
Daga bisani, wanda ya sace yaran ya kira iyayensu inda ya nemi kudin fansa har naira miliyan hamsin, amma bayan tattaunawa ya amince zai karbi naira miliyan ɗaya da dubu dari biyu.
Sai dai jami’an ‘yan sanda sun kitsa dabarar kama wanda ake zargi a wurin da aka tsara bayar da kudin fansar — a kusa da kwanar Farmers Motors a yankin jihar Bauchi.
Bincike ya kai jami’an zuwa Anguwan Rukuba a birnin Jos, Jihar Filato, inda suka samu damar ceto yaran lafiya kuma suka mika su ga iyayensu.
Daga baya, aka gano wanda ya aikata laifin mai suna Abdulkarim Tasiu, wanda ‘dan uwan mahaifin yaran ne, kuma ya amsa laifin yana mai cewa akwai tsohon sabani tsakaninsa da mahaifin yaran.
