Ƙarin wasu ƴan sanda 230 daga Kenya sun isa Haiti a wani ɓangare na nuna goyon baya ga dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (UN), wajen magance rikicin ƙungiyoyin ƴan daba da ke addabar ƙasar.
Maƙasudin zuwansu shi ne ƙarfafa yaƙi da ƙungiyoyin ƴan dabar da ke iko da mafi yawancin babban birnin ƙasar, Port-au-Prince, inda suke ƙara faɗaɗa mamayarsu.
A halin yanzu, an tura ƙusan dubu ɗaya na ƴan sanda daga Kenya zuwa ƙasar domin tallafa wa aikin. Ƴan dabar ana zargin su da aikata kisan ƙare dangi, fyade, da sauran laifuka masu muni.
Rikicin ya tursasawa kusan miliyan 1.5 na ‘yan Haiti tserewa da muhallansu, yayin da ƙasar ke fama da rashin tsaro mai tsanani.
