Ƴan bindiga da ke ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Unguwar Gada da ke ƙaramar hukumar Kafur ta jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Juma’a da safe, inda suka sace dabbobi da ba a bayyana adadinsu ba, tare da jikkata wasu mazauna ƙauyen mutum biyu.
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
A yayin harin, ƴan bindigan sun harbi wasu mazauna ƙauyen guda biyu, waɗanda aka bayyana sunayensu da Sani Yau da Umar Shamsu,Dukkaninsu sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga, kuma aka garzaya da su babban asibitin Malumfashi domin samun kulawar gaggawa.
Rundunar ƴan sanda tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro sun mayar da martani ga harin.
