Yan bindiga sun sake kai hari garin Goron Dutse dake karamar hukumar shanono a daren jiya Juma’a, sai dai jami’an soji dake yankin sun yi nasarar kashe 3 daga cikinsu tare da kwace baburansu, da kuma kubutar da wasu da suka yi yunkuri sacewa.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a biye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace barayin sun sace shanu 40.
Bayanai sun nuna cewa yan bindiga sun sake dawowa da safiyar yau Lahadi, a wani mataki na daukar fansa bayan kashe yan uwansu 3 a juya, har yanzu nahiyar mu tace ana bata kashi tsakanin sojoji da yan bindiga a karamar hukumar.
Mai Magana da yawun rundunar soji ta 3 dake nan Kano Manjo Zubair Babatunde ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.
Ya kara da cewa maharan sun fito ne daga Daurawa da Kira dake jihar Kano tare da shigowa Kano, kuma jami’an sojin da aka ajiye a a yankin yan kwada nan take suka tunkare su tare da samun nasarar.
