
’Yan bindiga sun kai hari a gidajen kwanan dalibai na Bilyaminu Usman Polytechnic, Hadejia, dake kan hanyar zuwa Malam Madori a Jihar Jigawa.
Rahotanni sun ce maharan sun daki wasu dalibai tare da kwace wayoyi masu yawa, sai dai yunƙurin da suka yi na sace wasu daga cikin daliban bai yi nasara ba saboda ihun neman agajin da suka rika yi.
Wani ganau wanda bai so a bayyana sunansa ba ya ce: “A kusan ƙarfe goma sha biyu na dare ne suka iso, suka tada hankali, suka ji wa wasu dalibai ciwo sannan suka kwashe wayoyi da dama na dalibai.”
Wani ganau na biyu, Tukur Danlami, ya ƙara da cewa: “Da ba don ihun da daliban suka yi ba, da ba zasu san abin da ya faru ba.
Da yake tabbatar da lamarin a ranar Juma’a, Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Jigawa, SP Shiisu Adam, ya ce: “sun samu rahoton harin kuma sun fara bincike tare da ƙara tsaurara matakan tsaro domin cafke waɗanda suka aikata.”
Adam ya bayyana cewa harin ya auku ne ranar Alhamis a wajen kwanan daliban maza na haya da ke wajen makarantar, amma ba nesa da ita ba.
Game da wurin, ya ce: “Wurin yana da nisa kadan kuma babu cunkoso, shi ya sa ya zama cikin sauƙi ga maharan su kai farmaki.”
Ya ƙara da cewa ’yan sanda da ke kusa sun ruga wurin bayan samun rahoto.
Ya kara da cewa daga cikin bayanan su dalibai biyu ne suka samu munanan raunuka kuma ‘yan sanda sun garzaya da su Asibitin Gwamnati na Hadejia domin samun magani.
Ya kuma ce bayan samun kulawa tuni aka sallame su.