Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina sun ce ƴanbindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, sun kuma kwashe mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara sun kuma hallaka akalla mutum 6.
inda suka sake kai wani hari a yankin karamar hukumar Dandume ta jihar.
Malam Ya’u Ciɓauna, mazaunin garin Layin Garaa na ƙaramar hukumar Funtua ya bayyanayadda lamarin ya faru
“Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ƴanmata da matan aure da kuma ƙananan yara har kimanin 53.
“Sun kuma kashe mutum 2 a Layin Garaa na ƙaramar hukumar Funtua da kuma wasu mutum 4 a garin Mai Kwama a cikin ƙaramar hukumar Dandume.” In ji shi.
Maigarin Layin Garaa, Mustapha Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, “mutane na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, kwatsam kuma sai ga wannan matsala ta harin ƴanbindiga”. In ji shi.
Hukumar ƴansanda a jihar Katsina ta ce tana kan bincike a kai lamarin, domin haka ba za ta ce komai ba sai ta kammala.
