
Rundunar ‘yan sanda shiyya ta daya dake nan Kano ta tsare fitaccen ɗan jaridar nan, Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, bayan wani ƙorafi da daraktan al’amuran gidan gwamnatin Kano Abdullahi Rogo ya shigar, yana zargin ɗan jaridar da bata suna.
Rogo dai yana fuskantar bincike daga hukumar EFCC da ICPC kan zargin almundahana da suka kai Naira biliyan 6.5.
Jaridar Daily Nigeria ta ce an cafke ɗan jaridar ne a ofishinsa dake nan Kano ba tare da an nuna masa takardar kamu ba, sannan aka wuce da shi kai tsaye zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta shiyyar domin amsa tambayoyi.
Majiyoyin Jaridar sun bayyana cewa ana tuhumar Danuwa Rano da laifin bata suna da kuma gudanar da gidan talabijin ta yanar gizo ba tare da lasisin hukumar NBC ba.
Sai dai Rano ya bayyana wa ‘yan sanda cewa mallakar gidan yanar gizo ko gudanar da shirye-shiryen intanet ba ya bukatar lasisin NBC, Amma duk da haka, ‘yan sanda sun cigaba da tsare shi.
Kawo yanzu dai Hedikwatar ‘yan sanda ta shiyyar ba ta fitar da wata sanarwa kan kama da tsare ɗan jaridar ba.