
Wasu Sojojin da haɗin gwiwar Hukumar (NDLEA), sun kama ‘yansandan bogi su biyu a mota kirar Hilux ɗauke da lodin tabar wiwi.
Lamarin ya faru ne Takum Junction, Wukari Local Government Area na jihar Taraba a tsakiyar makon Nan.
An samu nasarar cafke su ne a cikin Operation Lafiya Nakowa, wanda yake daƙile ayyukan laifi da ake yi harda ‘yan fashi da sauran masu aikata manyan laifuka a jihar Taraba.
A bayanan da aka samu daga rundunar Sojin, inda da NDLEA don kama mutanen biyu da suka yi shiga ta Mobile Police. Sun kasance cikin abin hawa biyu na Toyota Hilux da aka loda tabar.
Binciken farko ya nuna cewa mutanen ba ‘yan sandan gask bane.
Motocin kuma sun samo asali ne daga Akure, jihar Ondo, kuma suna kan hanyarsu ne ta zuwa jihar Adamawa.
An gano sama da kunshin sama da dubu daya na tabar daga motocin biyu.
Shugaban hadakar jami’an tsaron Brigediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa sojoji kan wannan wannan namijin aiki.