Binciken da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar a bana, ya nuna cewa akwai raguwar yawan mutanen da ke kamuwa da cutar tarin fuka (TB) a Najeriya, ciki har da jihar Kano.
Rahoton ya bayyana cewa sabbin matakan da hukumomi da abokan haɗin gwiwa ke ɗauka sun taka rawar gani wajen rage yaduwar cutar.
Hawan jini na kashe mutum miliyan 10 a duk shekara – WHO
MPD ta duba marasa lafiya fiye 500 da basu magani kyauta a Kano
Shugaban Hukumar Dakile Yaduwar cututtuka ta jihar Kano Dakta Sulaiman Musa, ya bayyana cewa “Nasarar da aka samu ba ta tabbata kai tsaye ba, sai da goyon bayan da gwamnatin Kano ke bayarwa ta fuskar kayan aiki da wayar da kan jama’a da kuma tallafawa cibiyoyin kula da masu fama da cututtukan.
“Da wannan ci gaba, har yanzu akwai bukatar ƙara azama wajen wayar da kan al’umma saboda da dama na cigaba da boye cutar ko kuma rashin kai kansu asibiti”. In ji shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga al’umma da su rika zuwa asibiti idan sun fara ganin alamomin cutar TB kamar tari mai ɗorewa fiye da makonni biyu, rama ba tare da dalili ba, da kuma gajiya ko zufa da dare.
