
Babban Hafsan Tsaro na Kasa, Janar Christopher Musa, ya bayyana goyon bayansa kan killace wuraren kiwo a matsayin mataki na rage rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da fulani a Najeriya.
Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a Abuja, a gabanin taron farko na manyan hafsoshin tsaro na kasashen Afirka, wanda aka tsara domin a karfafa hadin gwiwar tsaro da kuma fuskantar sabbin kalubalen tsaro.
Ya ce: “Kiwon shanu a killace zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro da ke addabar nahiyar Afirka, musamman rikice-rikicen manoma da makiyaya, wanda ke daya daga cikin manyan matsalolin tsaro da ake fuskanta.”
Janar Musa ya karyata rade-radin da ke yawo cewa yana goyon bayan kwace gonaki daga hannun mutane don kafa wuraren kiwo na gwamnati.
Za a gudanar da taron manyan hafsoshin tsaro daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Agusta, 2025, inda kasashen Afirka za su hallara don tattauna matsalolin tsaro da suka addabi nahiyar, tare da samar da ingantattun mafita a matsayin ‘yan uwa da ke da muradin wanzar da zaman lafiya a Afirka.