Daga Ahmad Hamisu Gwale
Dan wasa Ademola Lookman da Barbra Banda da kuma Ronwen Williams shiga jerin mutune uku da suka lashe manyan kyautuka a bikin fitar da Gwarazan Nahiyar Afrika na Hukumar Kula da Kawallon kafa ta Afrika na shekarar 2024.
Bikin zabar Gwarazan Nahiyar Afrika na shekarar 2024 ya gudana a ranar Litinin a birnin Marrakech din kasar Morocco da masu ruwa da tsaki a kwallon kafa a duniya duka halarta.
Ademola Lookman, na Najeriya ya lashe gwarzan dan wasan nahiyar afrika na Maza (CAF Player of the Year Men).
Sai kuma yar wasan Zambia Barbra Banda da ta lashe gwarzuwar yar wasan nahiyar afrika ta Mata (CAF Player of the Year Women).
Mai tsaran ragar kasar Afrika ta Kudu Ronwen Williams, shi ne ya lashe gwarzan mai tsaran raga na nahiyar afrika na Maza wato (CAF Goalkeeper of the Year Men).
Sauran wadanda suka lashe manyan kyautuka sun hada da Chiamaka Nnadozie ta Najeriya, wadda ta lashe gwarzuwar mai tsaran raga ta Mata wato CAF Goalkeeper of the Year Women).
Sai kuma shi ma Lamine Camara, na kasar Senegal, ya lashe gwarzan matashin dan wasa na Maza (CAF Young Player of the Year Men).
Ga jerin duka kyautukan da aka lashe.
Gwarzan dan wasan nahiyar afrika na Maza
(CAF PLAYER OF THE YEAR (MEN) Ademola Lookman (Nigeria / Atalanta)
Gwarzuwar nahiyar afrika ta Mata
(CAF PLAYER OF THE YEAR (WOMEN)
Barbra Banda (Zambia / Orlando Pride)
Gwarzan mai tsaran raga na Nahiyar Afrika na Maza
(CAF GOALKEEPER OF THE YEAR (MEN)
Ronwen Williams (South Africa / Mamelodi Sundowns)
Gwarzuwar mai tsaran raga ta nahiyar afrika ta Mata
(CAF GOALKEEPER OF THE YEAR (WOMEN)
Chiamaka Nnadozie (Nigeria / Paris FC)
Dan wasan nahiyar afrika na Maza da ke buga wasa a nahiyar ta Afrika
(CAF INTERCLUB PLAYER OF THE YEAR (MEN)
Ronwen Williams (South Africa / Mamelodi Sundowns)
Yar wasan nahiyar afrika ta Mata da ke buga wasa a nahiyar afrika
(CAF INTERCLUB PLAYER OF THE YEAR (WOMEN)
Sanaâ Mssoudy (Morocco / AS FAR)
Matashin dan wasan nahiyar afrika na Maza
(CAF YOUNG PLAYER OF THE YEAR (MEN)
Lamine Camara (Senegal / AS Monaco)
Matashiyar yar wasan nahiyar afrika ta Mata
(CAF YOUNG PLAYER OF THE YEAR (WOMEN)
Doha El Madani (Morocco / AS FAR)
Gwarzan mai horarwa na afrika na Maza
(CAF COACH OF THE YEAR (MEN)
Emerse Fae (Cote d’Ivoire)
Gwarzuwar mai horarwa ta Afrika ta Mata
(CAF COACH OF THE YEAR (WOMEN)
Lamia Boumehdi (TP Mazembe)
Tawagar nahiyar afrika ta Maza mafi kwazo
(CAF NATIONAL TEAM OF THE YEAR (MEN)
Cote d’Ivoire
Tawagar nahiyar afrika ta Mata mafi kwazo
(CAF NATIONAL TEAM OF THE YEAR (WOMEN)
Nigeria
Kungiya mafi kyau a nahiyar Afrika ta Maza
(CAF CLUB OF THE YEAR (MEN)
Al Ahly (Egypt)
Kungiya mafi kwazo a nahiyar Afrika ta Mata
(CAF CLUB OF THE YEAR (WOMEN)
TP Mazembe (DR Congo)
Alkalin wasa mafi kwazo a nahiyar Afrika na Maza
(CAF REFEREE OF THE YEAR (MEN)
Mutaz Ibrahim (Libya)
Alkaliya mafi kwazo a nahiyar Afrika ta Mata
(CAF REFEREE OF THE YEAR (WOMEN)
Bouchra Karboubi (Morocco)
Mataimakin alkalin wasa a nahiyar Afrika mafi kwazo na Maza
CAF ASSISTANT REFEREE OF THE YEAR (MEN)
Elvis Guy Noupue Nguegoue (Cameroon)
Mataimakiyar Alkaliyar wasa a nahiyar Afrika mafi kwazo ta Mata
(CAF ASSISTANT REFEREE OF THE YEAR (WOMEN)
Diana Chikotesha (Zambia)
Kwallo da aka ci mafi kyau a nahiyar Afrika
(CAF GOAL OF THE YEAR
Mabululu (Angola)
Jerin wasa 11 fitattu na Maza na nahiyar Afrika
Men’s FIFPRO CAF Best XI: (3-4-3 formation):
Andre Onana (GK) — Achraf Hakimi, Kalidou Koulibaly, Chancel Mbemba — Mohammed Kudus, Sofyan Amrabat, Franck Kessie, Yves Bissouma — Mohamed Salah, Victor Osimhen, Ademola Lookman.
Jerin yan wasa 11 na Mata fitattu na nahiyar afrika
Women’s FIFPRO CAF Best XI — (3-4-3 formation):
Andile Dlamini (GK) — Michelle Alozie, Karabo Dhlamini, Osinachi Ohale — Lebohang Ramalepe, Linda Motlhalo, Rasheedat Ajibade, Ghizlane Chebbak — Barbra Banda, Asisat Oshoala, Tabitha Chawinga.