Mai Magana da yawun gwamnan jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayar da tallafin naira miliyan 1 da dubu 200 ga Madarasatul Tahafizul Qur’an dake karamar hukumar Tofa.
Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayar da tallafin ne ranar Asabar yayin saukar karatun al’kur’ani na dalibai 22.
Gudunmawar kudin da ya bayar za a baiwa makarantar naira miliyan daya inda za a baiwa kowane malami naira dubu 20 yayin da dalibai masu sauka za a baiwa kowanne naira dubu 5000.
Wannan gudunmawa dai wani bangare ce ta bayar da gudunmawa wajen cigaban addinin musulunci.
Haka zalika Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bukaci daliban makarantar su cigaba da dagewa wajen neman ilimin addinin musulunci da na zamani don zama jakadu na gari.
Sauran wadanda suka bayar da kyauta yayin saukar akwai dan majlisar tarayya Tijjani Abdulkadir Jobe da ya bayar da naira dubu 150, shugaban karamar hukumar Tofa Yukubu Adis shi ma naira dubu 50 da sakataren karamar hukumar Adamu Mainasara da ya bayar da tallafin naira dubu 30.