Wakilan majalisar dokokin Amurka sun zo Najeriya domin ci gaba da tattaunawarsu kan matsalar tsaro.
Tawagar ta iso Najeriya ne a ƙarshen mako,

Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara Kan Tsaro saro, Nuhu Ribadu ne ya sanar da hakan a shafinta na X a ranar Lahadi.
“Zuwansu ya kasance wani ɓangare ne jerin tattaunawar da gwamnatin Najeriya ta yi da hukumomin Amurka a ziyarar da suka kai Washington a watan Nuwamba.
“Tattaunawar ta mu ta mayar da hankali ne kan dabarun yaƙi da ta’addanci da ƙara wanzar da zaman lafiya a Afirka da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu”. In ji shi.
Tawagar ta ‘yan majalisar ta ƙunshi Mario Díaz-Balart da Norma Torres da Scott Franklin da Juan Ciscomani da Riley M. Moore da kuma jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills.
A watan Nuwamba Ribadu ya kai irin wannan ziyara birnin Washington sakamakon zirgin kisan kiristoci da ake zargin Najeriya da Kuma furucin shugaba Trump na kawowa kasar hari Kan haka.
Majalisar Amurka ta yi zaman bin bahasi dangane da zargin tare jin ta bakin shugabannin Najeriya.
