Kungiyar SERAP ta shigar da shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas a kotu saboda kin bincikar zargin ‘yan majalisa bayara da cin hanci kafin su gabatar da kuduri
Karar ta biyo bayan wani faifan bidiyo da dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Ibrahim Auyo, ya yada inda ya ce ana karɓar tsakanin Naira miliyan 1 zuwa 3 domin a gabatar da kudiri ko koke a majalisar.
SERAP ta nemi kotu ta tilasta wa Akpabio da Tajuddin Abbas su mika lamarin ga hukumomin yaki da cin hanci don bincike da gurfanarwa.
Da kuma daukar matakan kare Ibrahim Auyo da ya fallasa zargin.
“Wannan zargi babban cin amanar jama’a ne da ya sabawa rantsuwar kama aiki”, in ji kungiyar.
Sannan ta kuma jaddada cewa bai kamata cin hanci ya zama sharadi wajen gudanar da ayyukan majalisa ba
