Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce ba abin mamaki ba ne idan ya fice daga jam’iyyar NNPP.
Jibrin, wanda ke daga cikin kusoshin Kwankwasiyya tare da kasancewa abokin siyasa na kusa da jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da DCL Hausa.
A cewarsa, ya isa ya yanke shawarar kansa a siyasa bisa abin da ya ga ya fi masa alherii.
“Ko jam’iyyar NNPP kanta ta bayyana cewa a shirye take don tattaunawa da sauran jam’iyyu. Don haka ba dole bane in tsaya a jam’iyyar. Ni dai na isa na dauki matsayar da na ga ta fi mini kyau,” in ji shi.
Jibrin ya ce tun kafin ya shiga Kwankwasiyya yana da kudi, inda ya zuba jarinsa wajen tallafawa tafiyar, wacce kuma ta taimaka masa ya samu nasara a majalisar wakilai a 2023.
Sai dai ya jaddada cewa ko da zai fice daga jam’iyyar, zai ci gaba da girmama Kwankwaso.
“Ko da ban kasance tare da Kwankwaso ba, ba zan taba zagin shi ba. Haka ma Ganduje, ban taba zagin shi ba duk da cewa mun rabu a siyasa. Ban taba neman kwangila ba duk da irin rawar da na taka wajen nasarar NNPP a Kano. Kwankwasiyya ta tsaya min, amma ni ma na tsaya mata,” in ji shi.
Ya kuma zargi cewa babu wani babban dan siyasar Arewa da ya tsaya masa lokacin da aka dakatar da shi daga majalisar wakilai a 2016, bayan ya zargi shugabannin majalisar da yin aringizo a kasafi.
Game da makomarsa a siyasa, dan majalisar ya ce:
“Komai zai iya faruwa. Zan iya ci gaba da zama a NNPP, zan iya komawa APC, PDP, ADC ko PRP. Zan iya zuwa inda na ga dama. Duk lokacin da na yanke shawara, zan bayyana matsayina.”
