Malam Ibrahim Shekarau ya ce, zai ci gaba da yin siyasa matuƙar yana raye.
Tsohon gwamnan Kano, Shekarau ya bayyana cewar siyasa wata babbar hanya ce ta hidima wa jama’a.
Tsohon Sanatan ya fadi haka ne yayin da yake hira da ’yan jarida a Kano a yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekaru 70 a ranar Laraba, ya kuma ce, ya gina siyasarsa ne bisa tafarkin addini da ɗabi’a.
“Siyasata addinina ce, addinina kuma siyasata ce. Shiga cikin tsarin samar da shugabanni na gari masu gaskiya hidima ce ga jama’a kuma wannan ibada ce a Musulunci.
“Matukar ina da ƙarfi, zan ci gaba da bayar da gudunmawa. A gare ni siyasa ba aiki ba ne da ake daina yi; nauyi ne na rayuwa gaba ɗaya,” In ji shi.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa, siyasarsa ba ta da nasaba da son kai, sai dai niyyar ganin an samar da shugabanni masu adalci da kishin al’umma.
Shekarau, wanda ya mulki Jihar Kano daga 2003 zuwa 2011, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su haɗa kai domin ƙarfafa dimokuraɗiyya, ya kuma yi kira ga shugabanni su mayar da hankali kan matsalolin rashin tsaro, talauci da yunwa.
Sannan ya yaba wa jam’iyyar PDP bisa juriyarta inda ya bayyana cewar har yanzu tana taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.
Ya kuma yi wa makomar siyasar Najeriya fatan alheri, tare da jadadda cewa zai ci gaba da goyon bayan kowace gwamnati don samar da zaman lafiya da jin daɗin ’yan ƙasa.
