Manajan daraktan hukumar kula da tashoshin jirgin ruwa, Alhaji Abubakar Dantsoho, ya bukaci a yi nazari game da tsarin tashoshin, tare da tabbatar da ganin an samar musu tsaron da ya kamata.
Manajan ya yi wannan kiran ne a yayin taron kungiyar jami’an hukumar, inda ya nuna cewa, nazarin zai tabbatar da samar da wadataccen tsaro, musamman ta hanyar kayan aiki na zamani a daukacin tashoshin jiragen ruwa kasar nan.
Ya kara cewa tsarin ISPS Code da ya fara aiki gadan-gadan a bara, zai taimaka wajen kara samar da tsaro a tashoshin, da kuma dakile duk wata barazana a wannan fanni.
A cewarsa, wannan mataki tamkar kira ne na fara zuba hannun jari domin kara habaka tsarin, wanda ba kawai bayar da kariya ga tashoshin jiragen ruwa ba, har ma da kare martabar kasar nan, wacce ta ke ita ce, uwa maba-da-mama ga sauran kasashen Afrika.
Ya kuma ce, shirye-shiyen wanzar da tsarin wanzar da tsaron na ISPS Code 2020, zai fuskanci kalubalen da ya hada da ayyukan ta’addanci, da ‘yan fashin teku, da safarar haramtattun kaya da sauransu.
Sai dai Abubakar Dantsoho, ya sanar da cewa, yanzu duniya na sauyawa, saboda haka hukumar ta ga ya kamata ta rungumi tsarin, tare da wanzar da shi gadan-gadan.