Gwamnatin tarayya ta alƙawarta sake ƙarfafa dakarun tsaron ƙasar domin magance matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a lokacin taron addu’o’i na musamman ga dakarun tsaron ƙasar da aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na ƙasa da ke Abuja.
Shettima ya yaba wa gudunmowar da sojojin ƙasar da suka mutu a bakin aikinsu na kare kima da mutuncin ƙasar, da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Masu Garkuwa da Mutane a Matsayin ’Yan Ta’adda
- ASUU Da Gwamnatin Tarayya Sun Kammala Sabuwar Yarjejeniyar
- Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da N2B Don Biyan Bashin Malaman Jami’a
An gudanar da taron addu’o’in ne a wani ɓangare na bikin ranar tunawa gudunmowar da dakarun tsaron Najeriya ke bai wa ƙasar.
Gwamnatin ƙasar ce ta ware ranar 15 ga kowane watan Janairu domin karrama dakarun tsaron ƙasar.
Kalaman mataimakin shugaban ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara samun barazanar tsaro a ƙasar, inda a yan kwanakin nan ma shugaban Amurka ya yi barazanar sake kai hari Najeriya.
