
Gwamnatin jihar Kano ta ce za a yada zaman da za yi da Sheikh Lawan Shui’aib Abubakar limamin masallacin Triumph kai tsaye a kafafen yada labarai domin cire shakku daga zukatan al’umma. Sakataren Majalisar Shura Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai a maraicen ranar Laraba.
“Za a fara da aikewa da malamin takardar gayyata wadda kuma za ta ƙunshi rana da lokacin da zai bayyana a gaban kwamitin.” Shehu Sagagi ya kuma ce, ba wai an dakatar da Triumph daga yin wa’azi ba ne kwata-kwata, an dakatar da shi ne daga tattauna batun da ake zarginsa da shi wanda ya janyo cece-kuce har zuwa lokacin kammala bincike.
Ya kuma kara da cewa, ba wai shi kaɗai majalisar Shura ta dakatar daga tattauna batun ba har ma da dukkannin sauran malamai da al’ummar gari. Inda ya yi kira da a kame daga tattauna batun har sai sakamakon binciken ya fito.