Hukumar shari’a Hukumar ta kano zata hada hannu da rudunar yan sada domin kawo karshen daba
Shari’a ta jihar Kano zata hada hannu da Rundunar Yan sanda domin kawo karshen fadace fadacen daba da kuma kwacen waya.
Shugaban Hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji ne ya bayyana hakan a lokacin da suka kai ziyara ofishin Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori domin kulla alakar aiki hadi da taimakawa, ta bangaren inganta tsaro a jihar.
Sheikh Daneji ya bayyana cewar sun kawo ziyarar ne domin hada hannu wajen fadakar da Matasa tare kuma da taimakawa rundunar ta Yansanda a bangarori da dama.
A jawabinsa Kwamishinan Yan Sanda CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana jin dadinsa bisa wannan ziyara, tare da bada tabbacin bayar da gudummawa ga Hukumar Shari’ar a dukkanin bangarorin da suke da hurumi akai, musamman bangaren yakar dabi’ar Fadace-fadacen daba da kwacen waya da ta addabi jihar a kwanakin nan.
A yayin ziyarar Sheikh Abbas Daneji yana tare da Kwamishina na 1 Gwani Hadi da na 2 Sheikh Ali Danabba da sauran Mambobi da Daraktocin hukumar.
