Zamfara: ‘Yan bindiga sun hana manoma girbe amfanin gona
Al’ummar garin Kairu da sauran wasu garuruwa fiye da goma na yankin ƙaramar hukumar Bukkyum a jihar Zamfara na cikin ƙaƙa-nika-yi sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da suka addabe su.Al’amarin da ya hana manoma girbe kayan amfanin gona, bayan sace mutum fiye da hamsin don neman kuɗin fansa daga garuruwan, kuma ala tilas mafi yawan jama’ar yankin sun yi gudun hijira zuwa wasu wurare.Wannan na zuwa ne duk da alƙawarin da gwamnatin jihar ta Zamfara ta yi na samar da matakan tsaro a yankin.An kwashe kimanin shekara goma ana fama da wannan matsala.Wani mutumin yankin, da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa BBC ce akwai garuruwa kamar 10 da har yanzu ba su isa su je gona ba.Ya shaida cewa ko a ranar Asabar sai da aka kwashe mutane kuma an hana su zuwa gonaki kwata-kwata.Manomin ya ce wannan yanayi na sanya su asarar milyoyin kuɗaɗe saboda rashin iya zuwa girbi, ga kuma barazanar fadawa cikin yunwa.Ya roƙi jami’an tsaro su taimake su saboda mutanensu sun warwatse, saukin da ake ganin kamar za a samu har yanzu ya gaggara, a cewarsa.Wannan lamarin dai ya haddasa wa jama’ar garuruwan asara mai dimbin yawa da tilasta wa mutanen garuruwan da abin ya shafa tserewa zuwa wasu garuruwa.