
Ibrahim Shekarau da sauran 'yan kungiyar siyasar Northern Democrats ND bayan kammala taronsu a Abuja
Ƙungiyar siyasa ta Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Malam Ibrahim Shekarau ta ce, za ta shiga sabuwar haɗakar ƴan hamayya ta National Coalition Group ƙarƙashin tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata David Mark domin tunkarar zaɓen 2027.
A wata sanarwar bayan taron da ƙungiyarda ta fitar a ranar Alhamis ta ce, duk da amincewar da ta yi na shiga haɗaka, za su ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tattaunawa yiwuwar kafa sabuwar jam’iyya ko kuma shiga wata jam’iyyar domin yin tafiya tare.

Kungiyar ta Northern Democrats ta ƙara da cewa sun amince da matsa wa gwamnati lamba musamman jagorancin majalisar dokoki wajen ganin an tabbatar da bin tsarin mulkin ƙasar sau da ƙafa.
ƙungiyar siyasar ta kuma kara da cewa, mambobinta sun amince su tattauna da jihohin arewacin ƙasar 19 dangane da halin-ko-in-kula da ake ciki dangane da yanayin da yankin yake ciki na talauci da rashin da aikin yi da kuma rashin tsaro.
Sanata Ibrahim Shekarau da kuma Sanata David Mark na daga cikin manyan jiga jigan jam’iyyar PDP a Arewacin Najeriya.