
Kungiyar ASUU ta yi barazanar maka Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) a gaban kotu, kan mummunar faduwar da daliban kudu-Maso-Gabas suka fuskanta a jarabawar UTME ta bana.
Shugaban ASUU reshen Jami’ar Nsukka Kwamared Oyibo Eze, ne ya bayyana haka yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Laraba a Nsukka, Jihar Enugu.
A cewarsa, yankin Kudu-Maso-Gabas ne ya fi fuskantar faduwar sakamako, yana mai zargin JAMB da shirya zagon kasa na hana yaran yankin samun damar shiga manyan makarantu a Najeriya.
“Wannan ba kuskure ba ne – wata manufa ce da aka kitsa domin danne hakkin dalibanmu.
“Idan JAMB ta kasa sake duba sakamakon tare da bai wa dalibai makin da suka cancanta, za mu dauki matakin doka nan take.” In ji Kwamared Oyibo.
Ya kuma bukaci gwamnonin yankin Kudu-Maso-Gabas da su dauki mataki cikin gaggawa domin kare makomar ‘ya’yansu, yana mai cewa rashin adalcin da ake nunawa daliban yankin bai kamata a lamunta ba.
ASUU ta ce tana da niyyar tura kwararru domin duba tsarin gudanar da jarabawar ta bana da kuma gano musabbabin faduwar da ta yi kamari a shiyyar, a wani yunkuri na kare sahihancin jarabawa da kuma makomar ilimi a yankin.