Gwamnatin Tarayyar ta tabbatar wa ‘yan kasa cewa tana daukar duk matakan da suka dace domin ceto daliban makarantar sakandare da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi.
Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya bayyana haka yayin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa Kebbi domin jajanta wa gwamnatin jihar da iyalan daliban da lamarin ya shafa.
Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni ga jami’an tsaro da su kara himma wajen tattara bayanan sirri da kuma daukar mataki cikin gaggawa don ganin an kubutar da daliban da aka yi garkuwa dasu.
Sanata Shettima ya bayyana wannan lamari a matsayin abin takaici, yana mai cewa har yanzu ‘yan ta’adda na kai hare-hare kan makarantun sakandare domin yin garkuwa da dalibai, a lokuta daban daban.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kebbi kan yadda take aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin ganin an kubutar da daliban ba tare da wata matsala ba.
A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya mika godiyarsa ga Sanata Shettima da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kulawa da daukar matakin gaggawa, yana mai bayyana cewa yana da kwarin gwiwa cewa gwamnatin tarayya za ta magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a jihar.
