
Daga Khalil Ibrahim Yaro
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA ta yi hasashen samun ambaliyyar ruwa da kuma Fari a kananan hukumomin sama da 18 a Jihar Kano.
Shugaban Hukumar Isyaku Abdullahi Kubarachi ne ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta gudanar a dakin taro na a Sansanin ‘Yan Yawon Bude Ido dake babban birnin jihar a ranar Alhamis.

A yayin gudanar da taron an tattaunawa yadda za a wayar da kan al’ummar don kare kansu daga afkuwar iftila’in da ake hasashen ne a damunar bana.
Hukumar ta kuma ce Takwas daga cikin kananan hukumomin a kwaryar birni suke, don haka akwai bukatar al’umma su dauki matakin yashe magudanan ruwa da tare da kwashe bola.
Shugaban Hukuma Isiyaku Abdullahi Kubarachi ya kuma ce, a kananan hukumomin Kano ta arewa da suka hada da Tofa da Bichi da Danbatta ne ake hasashen samun Fari a lokacin Kaka.
Kubaraci ya yi kira ga al’ummar yankin da su yi amfani da iri mai kyau wajen shuka wanda hakan zai taimaka musu wajen samun abinci da wuri.
A nasa jawabin Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Kasa mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Dakta Nuraddaeen Abdullahi wanda Sulaiman Sa’ad Abubakar ya wakilta ya ce, an shirya taron ne da nufin fadakar hukumomin masu ruwa da tsaki don kare afkuwar bala’o’i don tseratar da rayuka da dukiyoyin al’umma.
Bayan kammala taron a sansanin yawon bude ido na Kano, akai tattaki zuwa karamar hukumar Tofa daya daga cikin kana nan hukumonin da ake hassashen iftila’I da Fari a damunar bana,
Hukumar ta shirya taro wayar da kan al’ummar garin doka yadda zasu kare kansu daga afkuwar iftila’in.