Kasar Saudiyya za sake kawata masallatan Makka da Madina masu biyu da kuma fadadasu a cikin wannan shekara
Saudiyya za ta kashe sama da Dala biliyan 100 wajen sake kawata da kuma fadada masallatai masu alfarma na Makkah da Madinah
Jakadan Saudiyya a Najeriya Faisal bin Ibrahim Al ghamdi ne ya bayyana haka wajen bikin bankwana da wasu mutane 20 da kasar ta dauki nauyin su zuwa Hajj da umrah na wannan shekara.
A cewarsa, wadannan manyan ayyukan da suka hada da samar da karin kayan al’adu, tsarin kula da taron jama’a na zamani, da kuma sabbin fasahohi, suna nuna sadaukarwar Saudiyya wajen karbar bakuncin yawan mahajjata da ke ziyartar masallatan Makkah da Madinah kowace shekara.
“Shugabannin Saudiyya sun mayar da hankali sadaukarwa wajen yi wa alhazzai bakin Allah hidima. Wannan nauyi ne da muka dauka da gaske, kuma muna ci gaba da kokarin inganta bangarorin ibada a shirye-shiryen aikin hajji,” in ji shi.
Jakadan ya kuma ce, Masarautar Saudiyya ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da kudade domin kyautata da kuma bai wa mahajjata daga ko ina a duniya damar yin ibada cikin sauki.
“Shirin Martaba Masallatan Masu Alfarma ta hanyar daukar nauyin mutane daga ƙasashen duniya ya zama wata alama ta kokarin Masarautar Saudiyya na hada kan Musulmi a duniya da kuma saukaka musu damar ziyartar wurare mafiya tsarki a addinin musulunci.
“Hakan zai bai wa dubban mahajjata damar yin Umrah, inda ake daukar nauyin dukkan nauyinsu na tafiya da masauki da kuma sauran shirye-shiryen da ake bukata”. Inji Jakadan
Ya kuma jaddada muhimmancin bin dokoki da ka’idojin Masarautar da aka tsara don tabbatar da tsari da kuma tabbatar da lafiya da jin dadin mahajjata.