Gwamnatin tarayya ta ce za ta fara yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasarnan gwajin shan ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin.
Ma’aikatar ilimi haɗin gwiwar hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ne za su jagoranci aiki, kamar yadda wata sanarwa da hukumar NDLEAn ta fitar.
Hakan na zuwa ne bayan ganawar shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimi Olatunji Alausa.
Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren ƙasar nan.
Buba Marwa ya tabbatar da cewa gwajin ƙwayar zai shafi duka ɗaliban jami’o’in da sabbin da za su shiga.
Yayin da yake jawabi a wajen ganawar, Buba Marwa ya ce za su mayar da hankali ne kan makarantu waɗanda ya ce akwai miliyoyin yara da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimin ƙasa.
Buba Marwa ya ce rashin daƙile ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga wajen ƙananan yara ya taimaka wajen jefa matasan ƙasar nan cikin ayyukan ta’addanci da fashin daji da sauran miyagun ayyuka
