Hukumar alhazan Najeriya, NAHCON, ta ce ta yi kuskuren sanar da ranar 09 ga watan Yuni a matsayin ranar da za a fara dawo da alhazai gida Nijeriya
Hukumar ta ce a ranar 13/06/2025 za a fara jigilar alhazan zuwa gida bayan sun kammala aikin hajjin na bana.
Mataimakiyar darakta a sashen yada labarai na hukumar ta NAHCON Fatima Sanda Usara ta bukaci jama‘a su yi afuwa ga tuntuben alkalamin da ke kunshe a sanarwar da ta fitar tun da farko.
Za a fara jigilar ne da alhazan jihar Imo wanda kamfanin jirgin saman Air Peace ne zai mayar da su, sai Max Air da zai yi jigiliar alahazan jihar Bauchi, inda kamfanin Flynas zai yi jigilar na Jihohin Kebbi da Sokoto.
