
A yau Talata ne za a yi wa marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari jana’iza da misalin ƙarfe 2:00 na rana a mahaifarsa ta Daura da ke jihar Katsina.
Shugaban Nigeria Bola Tinubu ne zai tarbi gawar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a Katsina, domin yi masa jana’iza a Daura.
Gwamnan Katsina ya kuma bayar da tabbacin da ya samu daga shugaban Najeriya, Bola Tinubu cewa shi da wasu shugabannin ƙasashe biyu za su halarci jana’izar da za a gudanar a mahaifar marigayin da ke Daura.

Ya kuma bayyana cewa gawar marigayin za ta bar birnin Landan da misalin ƙarfe 6:00 na safiyar ranar Talata inda ake sa ran ta isa birnin Katsina da misalin ƙarfe 12:00 na ranar.
Tuni Kashim Shettima tare da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila suna birnin Landan inda za su rako gawar daga can zuwa Daura kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya yi ba da umarni.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ya kuma ce za a yi wa shugaban faretin ban girma a filin jirgin saman Katsina, kafin daga bisani a wuce garin Daura inda za a binne shi.
Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti na musamman da za su tsara jana’izar da kuma duk wani abu da ake buƙata wajen binne shugaba
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kafa kwamitin da zai jagoranci jana’izar ƙasa da za a yi wa tsohon shugaban ƙasar Muhamamdu Buhari.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin babban sakaten gwamnatin tarayya, Sanata George Akume zai jagoranci shiryawa tare da tsara yadda za a gudanar da jana’izar tsohon shugaban ƙasar.

Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnati, Segun Imohiosen ya fitar ya ce mambobin kwamitin sun haɗa da:
- Ministan kudi
- Ministan kasafi da tsare-tsare
- Ministan Tsaro
- Ministan yaɗa labarai
- Ministan ayyuka
- Ministan cikin gida
- Ministan Abuja
- Ministan Gidaje da raya birane
- Ministan kiwon lafiya
- Ministar al’adu
- Bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro
- Bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsare
- Babban mai taimaka wa shugaba kan harkokin siyasa
- Babban sifeton ƴansanda
- daraktan hukumar tsaro ta farin kaya
- Babban hafsan tsaron ƙasar.
Wakilanmu a garin Daura sun rawaito cewa tuni garin ya yi cikar kwari da manyan baki daga ciki da kuma wajen jihar Katsina don halartar jana’izar.