Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa rundunar yansandan jihohi, bayan kada kuri’a da aka gudanar a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Kafin a fara duba rahoton kudirin, dan majalisa mai wakiltar Birnin Gwari/Giwa a jihar Kaduna, Usman Zubairu, ya bukaci a ba yan majalisa karin lokaci domin nazarin takardar, yana mai cewa batun yana da matukar muhimmanci kuma ya kamata a yi nazari sosai.
Sai dai Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa an dade ana tattaunawa kan batun yansandan jihohi, kuma an yi cikakken nazari a kai.
Da yake gabatar da rahoton, Mataimakin Kakakin Majalisar kuma Shugaban Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, Benjamin Kalu, ya ce matsalar tsaro ta zama babban kalubale ga kasa, kuma kafa yansandan jihohi na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen inganta hukumomin tsaro ga abubuwan da ke faruwa.
Ya kara da cewa an gudanar da sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudirin, kuma ya samu gagarumin goyon baya daga sassa daban-daban na kasar.
Lokacin kada kuri’a, Kakakin Majalisar ya sanar da cewa za a yi amfani da kirga da hannu saboda na’urar kada kuri’ar lantarki ba ta aiki.
Yayin da ake kirga kuri’un, wasu yan majalisa sun nuna rashin amincewa da tsarin, suna ta maimaita cewa, “Wannan ba daidai ba ne.”
Bayan kammala kirga kuri’un, an bayyana cewa yan majalisa 289 sun kada kuri’ar amincewa da kudirin, yayin da dan majalisa daya ya kaurace wa kada kuri’a, ba tare da wani ya kada kuri’ar kin amincewa ba.
Amincewar Majalisar Wakilai na nufin kudirin ya samu wani gagarumin ci gaba a yunkurin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, yayin da masu goyon bayan sa ke ganin kafa yansandan jihohi zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar.
