
Rahoton arziƙi na shekarar 2025 ya yi hasashen cewa yawan ‘yan Afirka masu miliyoyin daloli zai ƙaru da kashi 65 cikin 100 nan da shekaru goma masu zuwa.
Bayanan da aka fitar, nahiyar Afirka a yanzu tana da attajirai 25 masu dala biliyan, mutum 348 da ke da aƙalla dala miliyan 100, da kuma mutum 122,500 masu dala miliyan ɗaya.
Kamfanin Henley & Partners, wanda ke sa ido kan harkokin arziƙi, ya bayyana cewa tattalin arziƙin Afirka ta Kudu da ƙasashen Hamadar Sahara zai bunƙasa da kashi 3.7 cikin 100 a shekarar 2025.
Wannan ya fi hasashen ci gaban Turai (0.7) da Amurka (1.4), inda ake sa ran Afirka gaba ɗaya za ta kai kashi 4.1 cikin 100 a 2026.
Afirka ta Kudu na ci gaba da rike ragamar attajiran nahiyar da kashi 34 cikin 100 na masu dala miliyan ɗaya, da adadin da ya kai mutum 41,100.
Wannan yawan ya kusan daidaita da jimillar attajiran ƙasashe huɗu da ke biyo bayanta: Masar, Morocco, Nijeriya da Kenya.
Rahoton ya nuna cewa ƙasashen guda biyar na da kashi 63 cikin 100 na masu dala miliyan ɗaya a nahiyar, tare da kashi 88 cikin 100 na masu dala biliyan.