Kungiyar Ecowas ta sanar da tura jami’an tsaro na ko-ta-kwana domin taimaka wa sojojin Jamhuriyar Benin, wajen kakkabe sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar da yammacin Lahadi, ta ce Shugaban ECOWAS, bisa ga amincewar shugabannin kasashen kungiyar, sun amince da tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Jamhuriyar Benin nan take.
Dakarun sun kunshi sojoji daga Najeriya da Saliyo da Cote d’Ivoire da kuma Ghana.
Sojojin za su taimaka wa gwamnatin kasar da kuma jami’an tsaronta wajen dakile dukkanin wata barazana ga wani yunkurin juyin mulki a nan gaba.
Bayanai sun tabbatar da cewa, an kama sojoji guda 13 waɗanda ke da hannu wajen kutse gidan talbijin din ƙasar da kuma sanar da juyin mulkin, ciki har da wani soja da aka kora a baya.
