
Hukumar Leƙen Asirin Soji ta Najeriya (DIA) tana gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna bisa zarginsa da ɗaukar nauyin sojoji da nufin kifar da gwamnatin Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai zargi mai karfi cewa tsohon gwamnan, wanda ɗan asalin yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas ne, ya ɗauki nauyin yunƙurin juyin mulkin, wanda da aka shirya aiwatarwa a ranar 25 ga watan Oktoba.
A ƙarshen mako ne jaridun Sahara Reporters da kuma Premium Times suka ruwaito cewa wasu hafsoshin soji 16, da Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sun shiga hannu saboda aikata abubuwan da ya saɓa ƙa’idar aiki, ana tsare da su ne a bisa zargin su da yunƙurin juyin mulki.
Daga cikin sojojin da aka kama akwai wani mai muƙamin Birgediya-Janar da wani Kanar da kuma wasu na ƙasa da su dake aiki a Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro.
Majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa akwai ƙamshin gaskiya a rahoton zargin yunƙurin juyin mulkin.