
Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da rufe kasuwannin Katarko, Kukareta da Buni Yadi a matsayin matakin gaggawa domin inganta tsaro a yankunan da ke fama da barazanar hare-haren ‘yan ta’adda.
Wannan mataki na ɗan lokaci ya biyo bayan rahotannin da ke nuna yiwuwar hare-hare daga ƙungiyoyin da ke tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas.
Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), Mai Ba Gwamnan Yobe Shawara Kan Harkokin Tsaro, ne ya sanar da haka.
“An yanke wannan hukunci ne domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyuka na musamman da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
“Rufe kasuwannin zai taimaka wajen dakile yaduwar ayyukan ta’addanci da kuma hana amfani da su a matsayin hanyar sadarwa ko tallafa wa masu tayar da hankali”. In ji shi.
Duk da cewa matakin na iya haifar da raɗaɗi ga ‘yan kasuwa da mazauna yankin, gwamnatin ta jaddada cewa tana aiki tuƙuru don rage tasirin hakan, tare da tabbatar da cewa za a buɗe kasuwannin da zarar an cimma burin tsaro.