
Hukumar FRSC ta ce haɗurran da ake samu a faɗin ƙasar nan ya ragu da kaso mai yawa, sakamakon sabbin tsare-tsaren da hukumar ta ƙaddamar don inganta tsaro a kan hanya.
Shugaban hukumar, Alhaji Shehu Mohammed ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Abuja.
Da yake karin bayani kan wannan cigaba, Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar a Kano, Abdullahi Labaran, ya shaida wa wakiliyar mu cewa, raguwar haɗurran ya samu ne bayan aiwatar da sabbin matakai da suka shafi wayar da kai, bin doka da amfani da fasaha wajen tuki.
“Tun bayan da hukumar ta bullo da sabbin tsare-tsare, musamman manhajar wayar hannu da ke koya wa direbobi dokokin hanya, an samu raguwar manyan haɗurra a sassa daban-daban na ƙasar,” in ji shi.
Ya kuma ce, hukumar ta fito da wata manhaja ta wayar hannu wadda kai tsaye direbobi za su san dokokin hanya da kuma ƙa’idojin tuki cikin sauki.