
Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare Ogugua Christopher a gidan gyaran hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Kasarnan.
Mai Shari’a Amina Adamu ce ta bayar da umarnin tsare mutumin yayin fara sauraron shari’ar, a ranar Talata.
Ana zargin Ogugua da mallakar gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba.
Sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki.
Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce ta gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su je kotun ba a ranar.
Bayan sauraron bukatar lauyan masu kara, Salisu Muhammad Tahir da na wanda ake karar, Gideon Uzo, Kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba.
Ana sa ran za a gurfanar da Christpher tare da sauran wadanda ake zargin a wannan Zama.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama Chrispoher ne bayan wani samame da jami’an hukumar ta NAPTIP suka kai gidansa da ke jihar Delta.
Sun kuma ceto yara takwas da ake zargin ya sace su daga Kano sannan ya kai su gidan marayun nasa da ke Asaba, babban birnin jihar ta Delta.