
Gwamnan Kano Audu Bako da Janar Yakubu Gowon da wasu manyan jami'an gwmanti na waccan lokaci
A rana mai kamar ta yau 27 ga watan Mayun 1967 Gwamnatin Mulkin Soja ta Janar Yakubu Gowon ta kirkiro Jihohi 12 Ciki har da jihar Kano.
Kwamishinan ‘Yansanda Audu Bako shi ne Gwamnan Jihar na Farko a Jihar kuma wanda ya shimfida ayyukan ci gaba da na raya kasa.
Babbar manufar Shugaba Yakubu Gowon na kikirkirar waɗannan jahohi ita ce, kusantar jama’a ga gwamnati da kuma kusanto da gwamnati ga jama’a.

A ranar 5 ga watan Mayu, 1967 Shugaba Gowon ya wargaza yankuna hudu na ƙasar Jihohi shida sun kasance daga tsohon yankin arewa. Su ne: Jihar Arewa maso Yamma, Jihar Arewa maso Gabas, Jihar Kano, Jihar Arewa ta Tsakiya, Jihar Benue-Plateau da Jihar Kwara.

Tsohon yankin yamma ya rabu zuwa Jihohi biyu: Jihar Yamma da Jihar Legas. Tsohon yankin tsakiyar yamma ya zama Jihar Yamma ta Tsakiya, yayin da tsohon yankin gabas ya dare zuwa Jihohi uku. Waɗannan su ne Jihar Gabas ta Tsakiya, Jihar Ribas da kuma Jihar Kudu-maso-Gabas.
Wannan jiha daga shekarar da aka ƙirƙire ta zuwa yau, ta samu jagorancin gwamnoni har goma sha 17 daga shekarar haihuwarta 1967 zuwa yanzu.

Wannan jiha na ɗaya daga cikin muhimman jihohin Najeriya, kuma kusan a yanzu ita ce cibiyar arewacin Najeriya ta fuskacin hada-hadar kasuwanci da siyasa. Ita ce jaha mafi yawan jama’a a duk faɗin Najeriya kamar yadda sakamakon ƙidayar jama’a da aka gudanar a 2005 ya tabbatar