Yau gidan Radio Premier ke cika shekara hudu cif-cif da soma shiryensa.
A ranar 11 ga watan Disambar shekara 2021 ne gidan radion ya soma yadda shirya-shiryensa a gida Mai lamba 5 kan Tintin Race Course a garin Kano.
Cikin lokaci kankani ya kai Daya cikin fitattun gidan radion da ake saurara a ciki da wajen jihar.
A ‘yan kwanakin da suka wuce gidan radion ya samu mabiya Miliyan Daya a shafinta na dandalin sada zumunta na Facebook.
Shin wane fata za ku yi mana?
