
Yau Najeriya ke Bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin Kai.
A ranar 1 ga watan Oktobar 1960 Najeriya ta samu ‘yancin kai daga kasar Britaniya wacce ta yi mata mulkin mallaka.
A kowacce shekara ana gudanar bukukuwan murna zagayowar wannan rana ciki har da faretin rundunonin sojojin ruwa da na sama da kuma na Kasa a Abuja.
Sai dai a wannan shekarar, Gwamnatin tarayya da dakatar da faretin ban girman da aka saba yi.
Sauran shagulgulan Bikin za su ci gaba. Ana Kuma sa rai Shugaba Tinubu zai yi jawabi na musamman ga jama’ar kasa a safiyar yau.
Tuni Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu a wannan rana domin murna zagayowar ranar.
Shin ko wane fata za ku yiwa Najeriya a wannan rana?