
Yau ce ranar dimokaraɗiyya a Najeriya, inda ƙasar ta cika shekara 26 akan tsarin mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.
Najeriya, ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka na bikin murnar ranar dimokuraɗiyya domin tunawa da zaɓen 12 ga watan Yuni wanda ake ganin shi ne zaɓe mafi inganci da aka taɓa gudanarwa a ƙasar.

Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya sauya bikin ranar dimokuradiyyar daga 29 ga watan Mayu (ranar da aka mayar da mulki hannun farar hula a 1999) zuwa 12 ga watan Yuni domin karrama wanda ake da yaƙinin shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar na 1993, Moshood Abiola.
Hakan na zuwa ne duk kuwa da cewa an soke zaɓen, lamarin da ya haifar da taƙaddama da ruɗani.
A kasar nan ta kwashe shekara 26 tana kan tafarkin mulkin farar hula ba tare da katsalandan na sojoji ba.

Sai dai bikin a wannan shekarar ya zo korafe-korafen yadda ake gudanar salon mulkin kasar a karkashi shugaba Bola Tinubu a wasu masu ‘yan kasar suka sha alwashin gudanar da zanga-zanga a fadin ƙasar.
Masu shirya zanga-zangar sun ce za su yi hakan ne domin kokawa kan matsin rayuwa da rashin tsaro da kuma “taƙaita ƴancin fadin albarkacin baki” da ake samu ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu.
Gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauki wasu matakai masu tsauri, kamar cire tallafin man fetur da sabbin manufofi na ɓangaren kudi wadanda ake ganin sun haifar da tashin farashin kaya da rage darajar naira, lamarin da ya jefa al’umma cikin matsin tattalin arziƙi.