 
        Sule Lamido ya bayyana taikaici da mamakin yadda ‘yan uwa abokan gwagwarmayar tabbatar da dimukradiyya a PDP suka juya masa baya.
Tsohon gwamanan na jigawa ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC a ranar Juma’a.
“Akwai matukar raini a matsayina na wanda na bai wa PDP da Najeriya gudummawa amma kuma a yi kokarin hana ni tsayawa Takara a jamiyyar da mu ka yi fama wajen kafuwarta”. In ji shi.
A martaninsa kan lamari, Sanata Ibrahim Shekarau da shi ma ake rade-radin tsayawarsa takarar shugabancin jam’iyyar, ya ce Sule Lamido bai sanar da su aniyarasa ta tsayawa ba, sai a karshen lokaci.
Ya kuma yi kira ga shugabbanin PDP da su bar kofa a bude ga duk wani dan jamiyyar dake da sha’awar tsayawa takarar wata kujera ta shugabancin jam’iyyar. Lamido ya korafin hana shia takara ta hanyara kin sayar masa da fom, ya kuma yi barazanar zuwa kotu kan haka. zar gin da jam’iyyatr ta musanta.

 
           
           
           
           
         
         
         
         
         
         
           
          