Wasu ‘yan siyasa a Kano na Shirin kai Ganduje, kara bisa yunkurin kafa kungiyar Hisbah mai zaman kanta.
Masu sukar tsarin na ganin ƙoƙarin na iya janyo tashin hankali.
Daga cikin wadanda su ka yi barazanar karar sun hada da tsohon Tsohon dan takarar gwamna, a jam’iyyar PDP Ibrahim Al-Amin Little.
“Yakama Ganduje ya janye wannan batu na kafa Hisbah mai zaman kanta saboda zaman lafiya” in ji shi.
Ganduje ya musanta zargin cewa tsarin zai iya haifar da fitina, jama’a ne ba su fahimci abin da ake ƙoƙarin yi ba.
