Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a damfara ta hanyar amfani da katin SIM da bayanan bankuna na jama’a.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba.
Ya ce an gano ƙungiyar ne bayan wani mutum mai suna Nura Abdullahi daga unguwar Kabuga ya kai ƙara cewa an sace masa layin waya, kuma daga bisani aka sace masa Naira miliyan 5 da dubu 750 daga asusun bankinsa.
Binciken da rundunar ta gudanar ya gano cewa, waɗanda aka kama suna amfani da bayanan BVN da NIN na mutane wajen buɗe asusun banki na bogi, samun katin ATM, sannan su kwashe kuɗin mutane ta hanyar damfara.
SP Kiyawa ya ce an samu wayoyin salula guda shida da kuma Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai (₦1.7m) a hannunsu lokacin da aka kama su.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa tawagar masu bincike bisa jajircewarsu da saurin ɗaukar mataki, tare da gargadin jama’a da su guji bayar da bayanan su na BVN da NIN ga waɗanda ba su amince da su ba.
Ya ƙara da cewa bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala bincike.
